Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: APC zata sha kaye matsuwar aka gudanar da sahihin zabe – Wike ga Buhari

Published

on

Gwamna Nyesom Wike, na jihar Ribas, ya bayana cewa jam’iyar APC zata fadi zabe, in har shugaban kasa Buhari yatabatar da an gudanar da zabe Mai inganci.

Indai Buhari yatabatar da cewa a gudanar da sahihin zabe, to tabas APC zata sha kaye a cewar gwamna Wike kamar yadda jaridar DAILYPOST ta rawaito.

Wike ya fadi hakan ne a gun taron kadamar da aikin titin Igwuruta internal dake karamar hukumar Ikwerre na jihar, Muna godiya ga shugaban kasa a bisa alkawari dayayi nacewa ba zai shiga harkokin zabe 2023 ba.

A cewar gwamna Wike ” Ina godiya ga shugaban kasa na son gani yaka fa tarihi a gudanar da sahihin zabe.

” Na gode ma Allah, shugaban kasa yace ba zai shiga harkokin zabe ba, hakan na nufi babu yadda jam’iyar shi zataci zabe.”

A ranar talata da ta gabata ne shugaban kasa yayi alkawari cewa zai tabatar da an gudanar da sahihin zabe a zabe Mai zuwa.

Yace ‘yan Nijeriya zasu damar zaben shuwagabanin su day kansu a kowane mataki.

Zafafa Labarai