Countdown
Connect with us

Siyasa

2013: Sanata Uba Sani ya lashe zaben fidda gwani takara Gwamna na jam’iyar APC a Kaduna

Published

on

Uba Sani yayin dayake jawabi agun zabe fidda gwani

Sanata Uba Sani, shine Wanda yayi nasara lashe zaben fidda gwani a tsakanin masu Neman takarar kujerar Gwamna Jihar Kaduna, Kar kashin inuwar jam’iyyar APC.

A jiya Alhamis ne dai aka gwabza zaben fidda gwani Yan takara kujerar Gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC a kasa baki daya, Cikin wanda suka gwabza a Kaduna sun hada da Hon. Sani Sha’aban, Alhaji Abubakar Bashir.

Sakamokon zaben sununa cewa Uba Sani, ya samu kuri’u 1,149 sai Alhaji Abubakar Bashir dake binsa abaya da Kuri’u 37, yayin da Hon. Sani Sha’aban ya tashi da Kuri’u 10, sai kuri’u 39 da suka lalace.

Uba Sani, shine Sanata mai wakilta Kaduna ta tsakiya a zauren majalisa a halin yanzu.

Nasara Uba Sani, a zaben fidda gwani yabashi damar tsayawa takara Gwamna a Kaduna a shekara 2023, kuma dama shine tan takara da Gwamna Elrufai, ya amince dashi.

A halin yanzu dai da Uba Sani, da Ashiru Kudan na jam’iyar PDP, ne zasu fafata a zaben 2023 kafin samun wasu ‘yan takara daga sauran Jam’iyu.

Zafafa Labarai