Countdown
Connect with us

Siyasa

2013: Hon. Isah Ashiru Kudan ya lashe zaben fidda gwani takara Gwamna na jam’iyar PDP a Kaduna

Published

on

Ashiru Kudan, yayin Ganawa da delegates kafin zabe

Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan, shine Wanda yayi nasara lashe zaben fidda gwani a tsakanin masu Neman takarar kujerar Gwamna Jihar Kaduna, Kar kashin inuwar jam’iyyar PDP.

A jiya laraba ne dai aka gwabza zaben fidda gwani Yan takara kujerar Gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a kasa baki daya, Cikin wanda suka gwabza a Kaduna sun hada da tsohon Gwamna Ramalan Yero, Sanata Shehu Sani, Sani Sidi da ma wasu.

Sakamokon zaben sununa cewa Ashiru Kudan, ya samu kuri’u 414, sai Sani Sidi dake binsa abaya da Kuri’u 260, sai Mukhtar Ramalan Yero, kuri’u 28, Bar. Sani Abas, 15, Haruna Saeed, 11, Shehu Sani, kuri’u 2, sai kuri’u 30 da suka lalace.

Nasara Kudan a zaben fidda gwani yabashi damar tsayawa takara Gwamna karo na biyu a jere, saidai a zaben 2019 yayi rashin nasara a hanu Malam Nasiru Elrufai, Wanda ya ba Gwaman maici yin mulki karo na biyu.

A yau alhamis, ake sa ran za a gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyar APC na masu ne Man takara kujerar Gwamna a fadin Nijeriya, kamala zaben ne zai bada damar sanin abokan gwabza wa Ashiru kuden a baben zabe shekara 2023 a Jihar Kaduna.

Zafafa Labarai